'NNPC bai miƙa $4 biliyan ga Nigeria ba'

Image caption Ministan mai a Najeriya, Dr Emmanuel Ibe Kachikwu.

Wani sabon rahoto ya ce kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya boye naira biliyan 824.7, kwatankwacin $4.2b, kudin mai da aka sayar, a watanni shidan farko na mulkin shugaba Buhari.

Rahoton wanda wata kungiya mai sanya ido kan albarkatun kasa wato Natural Resource Governance Institute, ta fitar, ranar Alhamis, ya ce kamfanin na NNPC ya sayar da mai na naira tiriliyan 1.24 wato $6.3b, a watanni shidan farko na 2015.

Rahoton ya kara da cewa kuɗaɗen da NNPC ya rike a watanni shidan na mulkin Muhammadu Buhari, sun fi wadanda kamfanin ya rike a 2013 da 2014, lokacin mulkin Goodluck Jonathan, da kaso 14.

Kungiyar mai sanya ido kan albarkatun kasa, ta ce alamu na nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba, duk kuwa da cewa shugaba Buhari, yana fafutukar kakkaɓe rashawa da cin hanci, a harkokin man ƙasar.

Kawo yanzu dai, kamfanin na NNPC bai mayar da martani ba.

A baya-bayan nan ne dai ofishin mai binciken kuɗaɗen gwamnatin Najeriya, ya ce gwamnati na bin kamfanin na NNPC naira tiriliyan 3.2, kuɗaɗen aka sayar da mai a 2014.

Sai dai kuma NNPC ya musanta yawan kuɗin.