Saudiyya za ta sa jarin $2tr don rage dogaro da mai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ƙasar Saudiyya ce kasa mafi girma dake fitar da mai a kungiyar OPEC

Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa za ta zuba jarin da ya kai dalar Amurka tiriliyan biyu a asusunta na zuba jari, domin rage dogaro da man fetur.

Asusun dai zai zamo shi ne irinsa na farko mafi girma a duniya.

Yarima mai jiran gado na biyu, Mohammed bin Salman ne ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Bloomberg shirin Saudiyyan na bunƙasa asusunta.

Wani babban ɓangare na shirin dai zai haɗa ne da sayar da hannayen jari na katafaren kamfanin mai na ƙasar wato Aramco -- Kamfanin da ya fi kowanne daraja a duniya.