Azerbaijan ta ce an hallaka sojojinta 12

Hakkin mallakar hoto Getty

Azerbaijan ta ce an hallaka 12 daga cikin dakaraunta, a arangama kan yankin Nagorno Karabakh, da mayakan 'yan aware ke rike da iko.

Fadan wanda aka yi amfani damanyan makaman atilare da kuma gurneti, ya barke tsakanin sojojin Azebaijan da 'yan awaren masu samun goyon bayan Armenia da sanyin safiyar Asabar.

Sai dai gwamnatin Armenia ta dora laifi ne akan yan Azerbaijan ta na mai cewa sun kaddamar da gagarumin farmaki tare da amfani da tankokin yaki da jirage masu saukar ungulu.

Shugaba Putin na Rasha ya yi kiran tsagata wuta nan take.

Rasha na sayar wa bangarorin biyu na Armenia da kuma Azerbaijan makamai.

Yankin Nagorno Karabakh da ake takaddama a kansa yan cikin Azerbaijan ne sai dai majalisar dokokin yankin ya kada kuri'ar hade wa da Armenia bayan rushewar tarayyar Soviet.