Shekara guda da kai harin Garissa a Kenya

Harin jami'ar Garissa a bara Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Fiye da mutane 100 aka hallaka a harin.

Al'umar kasar Kenya na bukin tunawa da kai hari a jami'ar Garissa, wadda ya yi janyo hasarar rayukan mutane 140 a shekarar da ta wuce.

Kusan mutane 100 ne suka taru a garin, dan yin addu'o'i ga wadanda suka rasu a lokacin.

Za kuma a gudanar da irin wadannan addu'o'i a birnin Nairobi da sauran sassan kasar.

A shekarar da ta gabata ne mayakan kungiyar al-Shabab suka far wa dalibai tare da hallaka su.