'Yan matan Chibok za su cika shekaru biyu

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar BBOG da ke fafutukar ganin an ceto 'yan matanan 'yan makarantar Chibok za ta gudanar da wasu shiye- shirye albarkacin cikon shekaru 2 da zagayowar ranar sace 'yan matan na Chibok .

Satar 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi.

Za a shafe mako daya a na gudanar da shirye shiryen da za su farawa tun daga ranar 8 ga wanan wata.

Daga cikin abubuwan da za gudanar sun hada da addu'oi a masanlatai da coci-coci da waazi da kuma zuwa fadar shugaban kasar Najeriya a ranar karshe.

Ya 'yan kungiyar za su fitar da sanarwa a gaban menama labarai domin sanar da duniya kudurin su