An gano kabari cike da gawawwaki a Palmyra

Birnin Palmyra
Image caption Dakarun gwamnati sun sake karbo birnin daga hannun 'yan IS.

Hukumomi a kasar Syria sun gano wani kabari da aka binne kusan mutane 40 a birnin Palmyra da dakarun kasar suka kwato daga hannun masu tada kayar baya na IS.

Wata majiya ta sojin kasar ta ce an gano gawawwakin sojoji da mayakan da ke marawa gwamnatin Syria baya dama a wurin.

Majiyar ta ce cikin gawawwakin har da na 'yan uwansu fararen hula da wasu yara uku, kuma ta yiwu ko dai an harbe mutanen ne ko kuma yanka su aka yi.