Darasi ga likita daga matukin jirgi

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

An kiyasta cewa mutane 7,500 na mutuwa a asibitotin kasashe masu amfani da harshen Inglishi duk shekara sanadiyyar kurakuran da aka iya kaucewa.

Daya daga cikin wadanda irin wanan lamari ya rutsa da su shi sanadiyyar irin wadannan kurakure shi Joshua Titcombe wanda ya mutu a babban asibitin Furness 'yan kwanaki bayan haifuwar sa a shekara 2008.

Wanan kuma sanadiyyar rashin daukar matakai daga likitocin game da gajiya da kuma numfashi da ya ke da gaggawa.

Mahaifiyar jaririn kuma ta mutu dan lokaci bayan ta haihu sanadiyyar kamuwa da wasu kwayoyin cuta.

Shi dai Jushua, jaririn an saka shi a cikin wata kwalba da ke da wayoyi a dan lokacin da ya yi a raye.

Idan akwai rahotanni da bincike na hakikan, za a iya daukar sabbin matakai da za su sa gujewa faruwar irin wadanan kurakurai.