Ya kamata Zuma ya yi murabus- Kathrada

Jacob Zuma Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Kathrada ya ce ya kamata Mr Zuba ya yi murabus.

Wani fitattacen dan siyasa karkashin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afurka ta Kudu Ahamd Kathrada ya bi sahun mutanen kasar da ke kiran shugaba Jacob Zuma ya sauka daga mukami.

A ranar Alhamis ne kotun kasar ta ce Mr Zuma bai mutunta kundin tsarin mulkin kasar ba ta hanyar yin biris da kiran da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar my suna Public Protector ta yi na ya dawo da kudaden gwamnati da ya kashe na gyaran gidansa a kauyen su.

Mr Kathrada wanda ya shafe kusan shekaru 20 a gidan kaso da ke tsuburin Robben tare da marigayi Nelson Mandela yace kasancewa Mr Zuma jagoran kasar, zai ragewa 'yan afurka ta kudu amincewar da suka yi da gwamnati.