Nigeria: An kama shugaban Ansaru

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kama Khalid al-Barnawi shugaban kungiyar Ansaru mai Ikrarin Jihadi.

Yana daya daga cikin mutane uku yan Najeria da Washington ta ayyanasu cikin jerin yan ta'adda na kasa da kasa a shekarar 2012.

Kakakin rundunar tsaro ta Najeriya Brigadier Janar Rabe Abubakar ya tabbatarwa da BBC cewa sojoji sun yi nasarar kama Khalid al Barnawi a garin Lokoja a ranar Juma'a.

Yace al Barnawi yana da cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Al Barnawi mai shekaru 47 wanda sunansa na ainihi shine Usman Umar Abubakar dan asalin garin Biu ne a Jihar Borno.

Shine babban wanda ake zargi ya jagoranci sace wa da kuma hallaka wasu turawa a lokuta daban daban.