Azerbaijan ta dakatar da bude wuta

Yankin Nagorno Karabakh Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yankin Nagorno Karabakh da ake takaddama akansa

Kasar Azerbaijan ta sanar da dakatar da bude wuta a kan fadan da suke yi da Armenia kan yankin Nagorno-Karabakh da ake takaddama akansa.

Ma'aikatar tsaro ta Armenia ta yi watsi da sanarwar inda ta ce ta jabu ce.

Mayakan Arminiyawa da ke samun goyon bayan gwamnati sun ce har yanzu sojojin Azerbaijan na ci gaba da kai masu hare - hare.

Bangarorin biyu na zargin juna da soma fadan da ya barke a ranar Asabar, tare da amfani bindigogin igwa da makaman artilary.

Sojoji akalla talatin aka kashe .

Yankin ya kasance karkashin ikon Arminiya 'yan a ware tun bayan da aka kawo karshen yakin da aka yi a shekarar ta 1994.