Zanga zangar kungiyoyin farar hula a Chadi

Image caption Kungiyoyin farar hula sun bayyana janyewar su daga cikin Hukumar shirya zabe mai zaman kanta.

Har a yanzu al'amurra sun kasa daidaita a kasar Chadi kasa da mako guda bayan da aka gudanar da zabe a kasar.

A yanzu haka kungiyoyin fararen hula sun bayyana janyewar su daga cikin Hukumar shirya zabe mai zaman kanta.

Kungiyoyin sun kuma jaddada cewa za su yi wani gangami na lumana a ranar Talata.

A wani bangare kuma kotu a kasar Chadi ta tsaida ranar 7 ga watan Afrilu domin sauraron shari'ar da ake yi wa wasu jigogin kungiyoyin fararen hula su hudu da aka tsare bisa ga zargin su da tada zaune tsaye da kuma bijire wa Hukuma.