Sani Aliyu Dandawo ya rasu a Yawuri

Sani Aliyu Dandawo Hakkin mallakar hoto Faruk Malami Yabo
Image caption Marigayi Sani Aliyu Dandawo na cikin mawakan kasar Hausa da suka fi shahara

Allah ya yi wa shahararren mawakin nan na kasar Hausa, Alhaji Sani Aliyu Dandawo, rasuwa.

Marigayin ya rasu ne ranar Lahadi a garin da ya girma, wato Yauri da ke jihar Kebbi, yana da kimanin shekaru 78.

Daya daga cikin 'ya'yansa Aminu Sani Dandawo ya shaida wa BBC cewa mahaifin nasa ya yi fama da cutar sukari ne tsawon watanni 10 kafin rasuwar tasa a gidansa da ke garin na Yauri, kuma tuni aka yi jana'izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci.

Alhaji Sani Aliyu Dandawo dai na cikin fitattun makadan fada wadanda suka dauki lokaci mai tsawo tauraronsu na haskawa a kasar Hausa, inda ya kwashe fiye da shekaru hamsin yana waka.