Ebola ta sake bulla a Liberia

Cutar ebola Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Cutar ebola

Hukumomin lafiya a Liberia sun tabbattar cewa an sake samun wani da ya kamu da cutar ebola, bayan da aka shafe tsawon watanni da kawarda annobar bakidayanta a kasar.

'Dan wata mata da ta rasu a baya bayanan sakamakon kamuwa da cutar ta ebola , ana yi masa jinya a wata cibiyar lafiya da ke Monrovia.

Hukomomi na gudanar da bicike a kan yadda matar da kuma 'ya yanta uku suka ketara cikin Liberia daga Guinea.

Liberia ta rufe iyakarta har zuwa wani lokaci, bayan da aka sake samun sabbin mutane da suka kamu da cutar ta ebola a kasar Guinea.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce tana da kwarin gwiwa cewa za a shawo kan batutuwan baya bayanan .