Arewa maso yammacin Nigeria ya fi talauci — Rahoto

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar kididdiga ta kasa ta fayyace talauci a jihohin Najeriya.

Wani bincike da aka gudanar na baya-bayan nan ya nuna cewa jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun fi ko ina fama da talauci a kasar, duk kuwa da cewa yankin ne yafi sauran takwarorinsa yawan jama'a.

Rahoton binciken ya bayyana cewa duk da yake akwai kokarin da aka yi na bunkasa tattalin arzikin yankin, amma watsi da aka yi da su a baya ya sa jama'ar yankin sun jima cikin talauci.

Rahoton dai wanda aka gabatarwa gwamnoni bakwai na shiyyar arewa maso yamma mai sama da shafi 70, ya yi dogon nazari kan matsalolin tattalin arziki da yankin na arewa maso yammacin Najeriya yake fama da su, inda ya fitar da alkaluma da ke nuna koma bayan yankin idan aka kwatanta da sauran shiyyoyin kasar.

Haka kuma rahoton ya nazari kan irin albarkatun da jihohin ke da su da za su iya cin moriyar su idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.

Sai dai a wani mataki na yukurin magance wannan matsala, gwamnonin yankin na arewa maso yamma sun ce sun dauki matakin shawo kan matsalar.

Masana dai na ganin ba wai maganar baki ta gwamnoni ce za ta rage matsalar ta talauci a jihohinsu ba, sai sun hada da kyakkyawan tsari da kuma yin aiki na gaske, sannan jama'ar su za su rabu da talaucin da ya addabi mafi yawan wadanda ake mulka.