Sojojin Syria sun kwato garin al-Qaryatain

Hakkin mallakar hoto epa

Kafar yada labaran gwamnatin Syria ta ce sojojin gwamnati sun sake kwato wani garin daga hannun yan kungiyar IS tare da taimakon jiragen yaki na Rasha.

Garin al-Qaryatain yana tazarar kilomita 120 daga yammacin birnin Palmyra wanda shima sojojin gwamnati suka kwato a makon da ya wuce.

Kungiyar sa ido da kare hakkin bil Adama a Syria wadda ke da mazauninta a Birtaniya ta ce sojojin shugaba Assad sun kwato fiye da rabin garin na al-Qaryatain sai dai kuma ana ci gaba da gwabza fada a wasu wuraren.