Mun fasa yin lullibi zuwa Iran — Air France

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin ya koma yin jigila zuwa Iran, bayan da aka dagewa Iran din takunkumin tattalin arziki.

Kamfanin jirgi na Air France ya ce ya sauya aniyarsa ta bin dokokin shiga kasar Iran, wadda ta nemi ma'aikatan jirgin mata da su rufe jikinsu, da zarar sun shiga kasar.

A watan da ya gabata ne dai kamfanin ya dawo da jigilar fasinjoji zuwa kasar ta Iran.

Tun da farko dai kamfanin ya tsaya kai da fata cewa dole ne ma'aikatansa mata su rufe jikinsu amma bayan da ya saurari korafin kungiyar ma'aikatan jirgi, ya sauya matsayinsa.

Yanzu haka manajojin na Air France sun ce ko dai a bar ma'aikatan su yi shigar da suke so ko kuma kamfanin ya janye jigila daga Iran.