Rikici ya barke a Congo

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Dennis ya yi tazarce a watan da ya gabata

Rahotanni daga Brazzaville babban birnin Congo sun ce ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga.

An cinnawa wani ginin ofishin 'yan sanda wuta a birnin.

Wani rahoto ya ce wani taron matasa sun sanya shingaye suna kuma wake-waken neman shugaba Denis Sassou Nguesso ya sauka daga mulki.

A watan da ya gabata ne aka sake zabar shugaban bayan wani zaben raba gardama da aka gudanar wanda ya yi gyara kan wa'adin shugabancin kasar da kuma adadin shekarun 'yan takara.