Chadi: Derby na fuskantar bore

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Idriss Deby na son yin tazarce a Chadi.

Ana ci gaba da takaddama tsakanin kungiyoyin farar hula da gwamnatin kasar game da tsayawa takara da Shugaban kasa da Idriss Deby ya yi.

A ranar Litinin ne 'yan sanda suka sa ke tsare wani shugaban kungiyar farar hula, Dokta Albissaty Saleh Allazam wanda shi ne mutum na 5 da ya ke hannun hukumomin tsaro a halin yanzu.

Ana dai zargin mutanen ne da yunkurin ta da zaune tsaye da kuma rashin mutunta dokar kasa.

Sai dai kuma kungiyoyin farar hular sun dage cewa za su fito a yau Talata domin yin zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da sake tsayawa takarar Deby shugaban kasa.