An yi dambe a majalisar jihar Nassarawa

Image caption Rikici a zaurukan majalisa a Najeriya ba sabon abu ba ne

'Yan majalisar jihar Nassarawa a Najeriya sun ba hammata iska a yayin wani zaman majalisar a ranar Litinin.

Rahotanni na cewa 'yan majalisar sun zage damtse a inda suka kai wa juna duka har da jifa da tebur a yayin rikicin.

'Yan sanda sun shiga tsakani a yayin da mai kula da sandar majalisar ya samu nasarar tsira da ita ba tare da wani lahani ba.

Kafofin yada labarai da suka rawaito lamarin sun ce nadin da gwamnan jihar Tanko Al Makura ya yi na kantomomin kananan hukumomin jihar ne makasudin rikicin.