Shirin Sanin Kai 2016: Yadda 'yan Najeriya ke saye da sayarwar gwal daga Dubai

Shirin Sanin Kai 2016: Me yasa 'yan Najeriya suke narka kayan yarin gwal a Dubai

Birnin Dubai yana tunkaho da kasancewarsa birnin gwala-gwalai, sai dai kuma da yawa daga mutane da suka hada da 'yan Najeriya, ba wai kawai suna zuwa Dubai din ba ne domin sayen kayan yari na gwal ba, har ma suna narka su sannan kuma a maida su zuwa sabbin nau'i.

Wadannan sarkokin gwal ne guda 22 a rataye da kuma warwaren gwal suke daukar idanu, a shagunan sayar da gwal da ke filin jirgin saman Dubai, daya daga cikin wurare masu yawan hada-hadar mutane a duniya. Iyalan Esochaghi, wadanda suke jiran jirginsu domin tashi zuwa birnin Lagos na Najeriya da karfe 2:25, bayan kammala siyayya, suna tsaye a bakin kofar shagunan.

" Wadannan sarkokin su ne abin da na fi so," in ji Ugochi Esochaghi, tana mai yin nuni zuwa ga taswirar malam bude mana littafi da ke kan kwadon sarkar da ke sanye a wuyanta. " Na saiwa 'yata ma daya," Sai ta yi murmushi, ita kuma Valeria wadda take koyon tafiya, tana tsotsar danyatsanta babba.

" Ni da iyalaina, mun dauki gwal wani abu mai matukar daraja. Tun ina yarinya nake amfani da shi, ina kaunar sa."

Saboda hasken da ke filin jirgin, hoton malam bude min littafin da ke kan kwadon sarkar wuyan Esochaghi, yana ta faman kyalkyali, ita kuma tana bayani kan zuwanta kasuwar gwal ta Dubai. " Mun kawo wasu daga cikin kayan yarinmu na gwal kuma an auna su. Sai a ka ba mu wasu gwala-gwalan masu nau'i daban domin mu zaba a ciki. Saboda haka sai a ka narka wadanda muka kawo domin dacewa da kirar da muke so.

" Ana yin kimanin kwana biyu, daga narkawa zuwa kira. Gwal din yana da kyau kuma ya fi na Najeriya araha."

Mijinta, Enyioha, wanda idanunsa,cikin zakuwa, suke kan agogon filin jirgin, ya yarda a dauke shi a hoto yana rike da kwalbar giya da ya siya, a shagunan da ke filin. Ita kuwa Esochaghi ta kasa boye murnarta. " Ba a ko'ina za ka samu wannan ba, abu ne na musamman saboda haka za mu kaiwa abokiyar arzikinmu kyautar sa."

Shin ya dace 'yan Najeriya su je Dubai domin sayen gwal?

" Kwarai, hakan ya dace," in ji Ugochi, lokacin da take tafiya zuwa hanyar fita. " Kawayena da dama suna zuwa nan. Abu ne da kowa ya ke yi." Birnin Dubai ya kwashe tsawon shekaru yana nuna kansa a matsayin wani wuri da masu yawon bude ido za su iya zuwa, a bara kadai, sama da mutane miliyan 14 ne suka ziyarci birnin kuma akalla sun kwana daya. Kuma sannu a hankali ana sanyawa mutane sha'awar gwal.

Sai dai kuma akwai wasu cibiyoyin saye da sayarwar na gwal kamar Indiya da China wadanda su ne manya. Majalisar harkokin gwal ta duniya, WGC ta ce kimanin kaso 30 zuwa 40 na yawan gwal a duniya, yana fitowa ne daga Dubai.

" Shekara 10 zuwa 15 da suka gabata, birnin Dubai ya zamo sananniyar kasuwar gwal. Tun a lokacin ne birnin ya yi suna da kasuwar saye da sayarwa," in ji John Mulligan, shugaban sashen masu sanya hannun jari na WGC.

Haraji a kan sayen gwal ba shi ne abu mafi mahimmanci ba, in ji Mulligan, aminci gwal da ke jan hankalin masu sanya hannun jari, shi ne a'ala. " Mai kyau ne gwal din. Idan kana sayen kayan yari, gwal yana da daraja a kan kansa. Saboda haka abu ne mai sauki fahimtar darajarsa."

Ugochi Akwiwu, wata marubiciya, ta yi min karin bayani kan kaunar da take da ita ga gwal, daga gidanta a birnin Benin na Najeriya. "'Yan Najeriya suna kaunar gwal kuma a yankin da nake alamu ne na nuna cewa mutum yana da arziki." In ji Ugochi.

" Asalina wani gari na kabilar Igbo da ke kudu maso gabshin Najeriya kuma al'ada ce yara su gaji gwala-gwalan iyayensu mata. Maza suna cin gadon kayayyaki da kasa, su kuma mata suna gadar gwal da atamfa 'yar kasar Holland."

Ugochi ta yi karin haske kan yadda ake sayen danyan gwal

  • Ka yi tayi sosai, ta haka ne ake sa ran za a sami farashin da ya fi da cewa.
  • Ka dauki fasfo dinka saboda masu sayar da gwal din za su bukaci ganinsa, sannan ka da ka manta da takardar sayen kaya, bayan da ka sayi gwal din.
  • Ka sayi gwal daga shagon da aka sani saboda za ka iya haduwa da masu sayarwa a kan hanya, ka da ka sai irin wannan.
  • Ka nemi sanin farashin gwal, a ranar da za ka saya.

Akwiwu, tana zuwa Dubai sau daya a shekara, kuma tana sayen dankunnen gwal ne. Tana saiwa kanta ne da 'ya'yanta. Amma mafi yawan mutane suna kasuwanci ne. " A lokacin da nake makaranta, wasu daga cikin 'yan ajinmu sun yi kudi ta hanyar sayen gwal daga Dubai su kuma sayar da shi a Najeriya.

" Kadan ne suka iya karasawa zuwa jami'a da ribar da suka samu. Farashin giram daya na gwal dai baya wuce $5, kuma ya fi araha a Dubai, akwai wanda ba ya son ragi ne?" Saboda tashin kudaden kasashen waje, banbancin farashin ka iya zama babba kuma akwai dama ga masu saye na hakika. Talutu Ahmed Olulana wadda take zaune a birnin Legas, tana harkar saye da sayarwar gwal. " Muna sayen giram daya na gwal a kan $5." in ji Talutu." Ina samun danyen gwal daga Afirka amma kuma ina sayen gwal din da aka sarrafa daga Italiya da Indiya da kuma Dubai.

"gwal abu ne mai cike da daraja saboda za ka iya safarar sa, ka kuma sayar da shi, sannan yana kara daraja. Gaskiya alamu ne na gane arzikin mutum."

Kamar Akwiwu, Talutu ba kawai ta mayar da gwal wanin abun saye d sayarwa ba ne, a wurinta "alamu ne na nuna sarauta. Sarakunan gargajiya da sarauniyoyi suna yin ado da abun da muke kira sarkin karafa wato gwal," In ji ta.

" Ni 'yar asalin jihar Kogi ce da ke shiyyar arewa maso tsakiyar Najeriya, kuma bisa al'adarmu, muna ba wa mallakar gwal mahimmancin gaske. A mafi yawancin sassan jihata, dole ne mace ta mallaki gwal kafin ta yi aure."

Motoci masu gudu da jirage masu tsada ka iya lalacewa, amma shi kuwa gwal zai zamo yana nan har abada, musamman ga 'yan Najeriya.