Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 60 a Pakistan

Image caption Pakistan na yawan fama da ambaliyar ruwa
Jami'ai sun ce a kalla mutane 60 ne suka mutu sakamakon gagarumar ambaliyar ruwa a arewa maso yammacin Pakistan.

Rahotanni sun ce mace-macen sun fi yawa a yankin Khyber Pakhtunkhwa, amma kuma al'amarin ya shafi wasu bangarorin yankin Kashmir da Gilgit Baltistan ma.

Duk da cewa damina bata kankama ba, amma ruwan sama na farko-farko ya yi barna a kauyukan Pakistan inda basu da ababen more rayuwa.

Jami'ai sun ce an gargadi mutanen karkara da su bar kauyukansu zuwa wuraren da ake tunanin abin ba zai shafa ba.

A shekarar da ta gabata fiye da mutane 170 ne suka mutu a Pakistan sakamakon tsananin ruwan sama.

Karin bayani