'Yan Afirka masu safarar kuɗaɗe — Rahoto

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A 2012 ne Birtaniya ta tsayar da asusun kudaden James Ibori da sun kai $37m

Sunan tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya, James Ibori, ya bayyana a cikin jerin sunaye 'yan Afirka 18 da wasu takardu na bayanan sirri suka bayyana yadda wasu masu mulki na duniya ke safarar kuɗaɗe da kaucewa biyan haraji.

Wani kamfanin lauyoyi na Panama da ke gudanar da ayyukansa a asirce, wanda kuma ya taimakawa wasu daga cikin shugabannin aiwatar da miyagun dabi'un nasu, ne ya fidda bayanan na sirri.

Takardun sun bayyana alaƙar Ibori da kamfanonin mai guda huɗu, a inda aka yi amfani da ɗaya daga ciki wajen sayen jirgin alfarma na $20m.

Daman dai an kama mista Ibori da irin wannan laifi a 2012, a Ingila.

Sauran mutanen da suka bayyana a takardun sun haɗa da Khulubuse Zuma wanda ɗa ne a wurin shugaban ƙasar Afrika ta kudu da kuma tsohon shugaban ƙasar Sudan Ahmad Ali al-Mirghani da tsohon mataimakin alƙalin alkalai na Kenya, Kalpana Rawal da kuma Kojo Annan wanda ɗa ne ga tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan.

Takardun, waɗanda wata jaridar Jamus ta samu wanda kuma BBC ta gani sun nuna cewa kamfanin Mossack Fonseca, ya taimakawa mutane daga sassa daban-daban na duniya kafa kamfanoni a waje da nufin kaucewa biyan haraji.