Kenya: Za a cigaba da shari'ar Ruto

Hakkin mallakar hoto DPPS Kenya
Image caption Mataimakin shugaba Kenya William Ruto

A ranar Talata ne za a cigaba da shari'ar da kotun hukunta manyan laifukan yaki na kasa da kasa ta ke yi wa mataimaikin shugaban Kenya William Ruto da wani jarida Joshua Sang.

Mutanen biyu sun musanta tuhumar da da ake yi musu na aikata manyan laifukan yaki tare da kisan mutane 1,200 bayan da aka gudanar da zaben shekara ta 2007 a Kenya.

Ana sa rai kotun za ta yi watsi da karar ko kuma ta ci gaba, yayin da lauyoyinsu masu kare wadanda ake zargi ke cewa tuhume-tuhumen babu hujja, mai gabatar da kara kuwa na cewa suna da isassun hujjoji.

Ana zargin Mista Sang da amfani da shirinsa na rediyo wajen shirya kai hare-hare a bayan zaben da aka yi a kasar

Mista Ruto na adawa ne da Kenyatta kafin zaben amma suka yi wani kawance da ya kai su ga lashe babban zaben a shekara ta 2007.