An cire manhajjar Taliban daga Google

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Rahotanni sun ce an cire manhajar saboda ta saba ka'idojin kamfanin Google

An cire daga rumbum manhajoji na wayoyin tafi da gidan ka manhajar Alemarah da kungiyar Taliban ta kirkiro.

Tun da farko ana wallafa bayanai ne a manhajar Alemarah cikin harshen Pasto tare da fitar da bayanai da faya fayen vidiyo na kungiyar Taliban da ke Afghanistan.

Kungiyar dai ta ce an cire manhajar saboda tangarda da aka fuskanta ne jim kadan bayan da aka kaddamar da ita a ranar daya ga watan Afrilu.

Sai dai BBC ta fahimci cewa an cire manhajar ce saboda ta saba wa ka'idojin kamfanin Google da suka haramta sanya kalaman batanci a manhajojin kamfanin.