Saura kiris na bar buga leda — Rooney

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun watan Fabrairu, Rooney bai kara buga wasa ba.

Kyaftin din Ingila kuma dan wasan gaba na kulob din Manchester United, Wayne Rooney, ya ce 'yan shekaru kadan suka rage masa, a harkar wasan tamaula.

Rooney wanda ya zura kwallaye 7 a wasannin neman gurbin shiga gasar Euro 2016, bai kara buga wasa ba tun watan Fabarairu saboda raunin da ya samu a gwiwarsa.

Dan wasan ya ce " har yanzu ina da sauran 'yan shekaru, kamar yadda nake ji a jikina. A har kullum ina tunanin abin da zai zo a gaba sannan kuma ina kokarin ganin na yi iya bakin kokarina."

'yan wasan da suka fi zura kwallaye a gasar Premier ta bana dai dukkansu 'yan wasan gaba ne na kungiyar wasan Ingila wato Harry Kane da Jamie Vardy.