Attajirai ba sa biyan haraji — Rahoto

Image caption An gano cewa har da na hannun damar shugaban Rasha a badakalar

Wasu takardu na bayanan sirri da aka samu sun bayyana yadda wasu attajirai da masu fada aji na duniya ke amfani da dukiyarsu wajen kaucewa biyan haraji.

Takardun sun alakanta shugabannin kasashe 72 wadanda ke kan mulki a yanzu ko kuma suka sauka, da hannu a wani kamfanin lauyoyi na Panama da ke gudanar da ayyukansa a asirce.

Kamfanin ya kuma taimaka wa wasu masu hulda da shi wajen safarar kudade da kaucewa biyan haraji da kuma kaucewa takunkumin kasa da kasa.

Daga cikin wadanda aka bayyana cewa suna da hannu dumu-dumu har da wasu na hannun damar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Takardun, wadanda wata jaridar Jamus ta samu wanda kuma BBC ta gani ya nuna cewa kamfanin Mossack Fonseca, ya taimaka wa mutane daga sassa daban-daban na duniya kafa kamfanoni a waje da nufin kaucewa biyan haraji.

Mossack Fonseca ya ce kamfanonin halastattu ne kuma ya gudanar da ayyukansa ne bil hakki da gaskiya, sai dai kamfanin ya ce yana nadamar amfani da harkokinsa wajen gudanar da wani abu da ba daidai ba.