Iran ce gaba a hukuncin kisa — Amnesty

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu matasa da aka yankewa hukuncin kisa a Iran, bisa yi wa kananan yara maza fyade.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'ada ta Amnesty International ta ce an samu karuwar mutanen da ake yanke wa hukuncin kisa bara, mafi girma da aka taba samu cikin shekaru da dama.

Kasashen Iran da Pakistan, da kuma kasar Saudiyya sune suka zartar da kashi casa'in cikin dari na mutane dubu daya da dari shida da talatin da hudu da aka zartar musu da hukuncin kisan.

Adadin bai hada da kasar China ba wacce ake ganin ta fi kowace kasa a duniya zartar da hukuncin kisa amma bata bayyana haka ga kasashen duniya.

Kasar Iran dai ta zartar da hukuncin kisa kan kusan mutane dubu da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi, cikin su har da kananan yara hudu da aka samu da laifi.