An haramta sayar da barasa a India

Image caption Sahun mata masu zanga-zanga a India domin neman a hana shan barasa

Jihar Bihar da ke Indiya ta haramta sayar da giya, a gidajen cin abinci da otal-otal da kuma wuraren shan giya.

Haramcin wanda zai fara aiki nan take, ya biyo bayan wani taƙaitaccen haramcin da aka sanya a kan sayar da barasar gargajiya, a makon da ya gabata.

An sanya haramcin ne dai saboda koken da mata ke yi na irin cin zarafin da mazansu masu kwankwaɗar barasa suke yi musu.

A baya dai jihohi da dama sun sanya irin wannan haramcin a kan sayar da giya amma daga baya suka janye saboda la'akari da asarar da gwamnati take yi wajen samun kuɗin shiga.