ICC:Ana yin katsalandan a al'amuran shaidun Ruto

Fatou Bensouda babbar mai gabatar da kara ta kotun ICC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fatou Bensouda babbar mai gabatar da kara ta kotun ICC

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta ICC ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto.

Alkalan kotun sun kafa hujja da cewar ana yin katsalandan a cikin al'amuran shaidu kuma siyasa ta shiga cikin lamarin.

Ana dai tuhumar Ruto tare da wani dan jaridar ƙasar, Joshua Sang bisa zarginsu da hannu a kisan mutane 1200 a rikicin bayan zabe na 2007.

Dama lauyoyinsu sun nemi kotun ta ICC da ta yi watsi da shari'ar bisa rashin shaida, sakamakon sauya matsayi da shaidu suka yi, duk da cewa mai gabatar da karar a kotun, Fatou Bensouda ta kafe cewa akwai isassun shaidu.

Shugaban kasar, Uhuru Kenyata ya bayyana farin cikinsa, inda ya ce shi dama tun farko ya san mataimakin nasa bashi da laifi.

A shekarar 2014 ma Kotun ta yi watsi da irin wannan tuhumar da aka yi wa shugaba Uhuru Kenyatta.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International dai ta ce duk da kasancewar haka, dole ne a tabbatar da an kwato hakkin wadanda suka fuskanci cin zarafi bayan tarzomar zaben da aka gudanar a shekarar 2007 da 2008.