Firayin ministan Iceland ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firayi ministan shi ne babban na farko da ya yi murabus, sakamakon kwarmata bayanai daga kamfanin na Mossack Fonseca.

Firayiminstan Iceland, Sigmundur Gunnlaugsson ya yi murabus, inda ya kasance wani babba na farko da kwarmata bayanai daga kamfanin Mossack Fonseca, ta sa ya rasa mukaminsa.

Bayanan da aka kwarmata, sun nuna cewa Mista Gunnlaugsson da matar sa, sun mallaki wani kamfani a kasar waje mai suna, Wintris, kuma bai bayyana hakan ga majalisar dokokin Iceland din ba.

Ana zargin mista Gunnlaugsson ne da boye kadarori na miliyoyin daloli.

Sai dai ya ce ya sayar da hannayen jarin shi ga matarsa, a don haka bai aikata ba dai-dai ba.

Fitattun mutane a duniya da suka hada da shugabannin kasashe fiye da 70, masu ci da tsaffi ne aka gano suna da alaka da kamfanonin kasashen waje, a bayanan da aka kwarmata.