Nigeria: Yara masu kurumta na bukatar taimako

Kananan yara a Najeriya
Image caption Kananan yara a Najeriya

A Najeriya wata kungiya mai yaki da kurumta a tsakanin kananan yara ta bukaci gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen samar da kayan aiki.

Ta ce ta hakan ne za a iya yi wa yaran da ke da matsalar kurumtar da za a iya magancewa aiki a asibitoci, da kuma daukar nauyin yi wa wasu yaran da ke bukatar aiki na zamani don gyara musu jinsu.

Kungiyar wacce galibi iyayen yara masu larurar kuramta suka kafa, ta kuma kunshi wasu da ke da muradin tallafa wa mata wajen wannan fafutuka ta nema wa ire-iren kananan yaran da za a iya magance musu matsalolin.

Shugabannin kungiyar sun gabatar da bukatun nasu ne ga ministan lafiya na Najeriyar Farfesa Isaac Folowunsho Adebowale, a yayin ziyarar da suka kai masa ma'aikatar lafiya ta kasar, don ganin gwamnati ta dauki matakan taimaka wa kuramen yaran.

Sun ce muddin hukumomin suka taimaka, za a iya yi wa yara da yawa da ke fama da kurumtar da za a iya magancewa aikin da za su rika ji kamar sauran yara.

Ministan ya bukaci kungiyar da ta gabatar da bukataun nata a ruubuce, ta yadda gwamnati za ta duba yadda za ta tallafawa kananan yaran masu fama da matsalar kurumta.

Ya kuma ce gwamnatin za ta sa ya zama doka duk wani asibitin gwamnatin tarayya ya dauki tafintar kurame marasa lafiya don a rika fahimtar su.