NEMA ta kai tallafi makarantar marayu a Kano

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption NEMA ta kai kayan abinci da tufafi da kuma wasu kayan bukatu ga yaran su 100.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nigeria NEMA ta bada tallafi ga makarantar marayun jihar Borno da rikicin Boko Haram ya raba da iyalen su, wacce ake gudanar da ita a Kano.

Hukumar ta kai kayan abinci da tufafi da kuma wasu kayan bukatu yau da kullum a matsayin gudummuwa ga yaran su 100 da yanzu haka suke hannun gwamnatin Kano.

A yanzu haka dai gwamnatin ta Kano ta ce tana shirin karo wasu yaran 100 dan hada su da marayun da ke jihar.

Gwamnatin jihar Kano ce ta bude makarantar inda ta dauki alkawarin daukar nauyin rayuwar marayun.