Za a farfado da masana'antun tufafi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Farfesa Osinbajo ya ce yana da kyau 'yan Najeriya su dinga sayen tufafin da ake yi a kasar

Mataimakin shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce sayen kayayyakin da ake sarrafawa a gida zai farfado da masana'antun tufafi a kasar.

Farfesa Osinbajo ya yi wannan magana ce a fadar shugaban kasar yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar masana'antun tufafi da kuma mambobin kwamitin tabbatar da aiwatar da manufofin farfado da masana'antun sarrafa tufafi.

Ya ce, "Sayen kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya da 'yan kasar za su yi ya wuce don su sanya tufafin da ake yi a kasar kawai, al'amari ne da yake da muhimmanci ga tattalin arziki da kuma walwalar al'umma."

Tun da fari dai mambobin kwamitin tabbatar da aiwatar da manufofin farfado da masana'antun sarrafa tufafin, sun samar da dabarun farfado da masana'antun da ke sarrafa auduga da tufafi, wadanda suka hada da karfafawa mutane gwiwa wajen amfani da tufafin da ake yi a Najeriya.

A saboda haka ne ma kwamitin yake son ware wata rana guda mai taken "Wear Naija Day," wato "ranar sanya tufafin da aka yi a Najeriya," inda dukkan ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni za su sanya kayan da aka yi su a kasar.

Gwamnati na kokarin ganin ta gabatar da wani sabon tsari na farfado da masana'antun ta hanyar yakar fasa kwabri don a samu raguwarsa da kashi 15 cikin 100 zuwa shekara mai zuwa.

Kazalika, gwamnatin na kokarin samar da kudade ga wannan bangare da kuma shawo kan matsalar wutar lantarki.