Nigeria: Ana ci gaba da shari'ar Saraki

Image caption A watan da ya gabata ne Sanata Saraki ya bayyana a gaban kotun bisa rakiyar dumbin matasa

A ranar Talata nan ne ake ci gaba da shari'ar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, a kotun da'ar ma'aikata.

Ana dai tuhumar Saraki ne da yin karya wajen bayyana adadin kadarar da ya mallaka, zargin da ya musanta.

A ranar Litinin ne kuma sunan iyalan Bukola Sarakin dai ya bayyana, a jerin sunayen da takardun da wani kamfanin sirri na Panama ya fitar.

Takardun na sirri dai sun yi zargin cewa Saraki bai bayyana wasu kadarori guda hudu mallakar 'yan uwan matarsa masu alaka da man fetur.

Sai dai kuma Bukola Saraki ya musanta aikata ba dai-dai ba, domin a cewarsa kadarorin mallakar iyalinsa ne kuma dokar Najeriya ba ta nemi da ya bayyana abubuwan da iyalan matarsa suke da su ba.