Nigeria: Ya za a magance matsalar man fetur?

Image caption Dogayen layukan mai a gidan mai a Najeriya.

Masana harkokin tattalin arziƙin ƙasa dai na cewa zai yi kyau ƙasar ta yi koyi da matakan da ƙasar Sudan ta yi amfani da su wajen magance matsalolin man fetur.

Alhaji Shua'ibu Idris, masani ne kan tattalin arziki ta fuskar albarkatun ƙasa, ya kuma shaidawa BBC cewa idan har ana son kawar da matsalar ƙarancin mai a Najeriya dole ne sai an dauki matakai guda uku:

  • Faɗaɗa matatun mai sannan kuma a sake sabunta su.
  • Sanya kananan matatu da ke tace mai na wucin-gadi kamar guda biyar wadanda kuɗin kowacce bai wuce $1b ba.
  • Gwamnati ta cire hannunta daga harkar mai domin ba wa 'yan kasuwa dama su shiga a dama da su.

Domin jin cikakken bayani da masanin ya yi kan magance matsalar, saurari hirarsa da wakilinmu na Legas, Umar Shehu Elleman:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Image caption 'Yan bunburutu suna cin kasuwa a Abuja Najeriya.

Ƙarancin man fetur na ƙara tsananta, a sassa da dama na Najeriya, inda wasu masu ababen hawa ke kwana a kan layi, a gidajen mai.