Zuma ya tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana tuhumar Zuma da amfani da kudin gwamnati wajen gina gidansa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya tsallake wani yunkuri na majalisar dokokin kasar na tsigeshi daga mukaminsa.

Shugaban ya samu goyon bayan 'yan jam'iyyarsa ta ANC wacce ke da rinjaye a majalisar.

'Yan adawa a majalisar dokokin ne suka gabatar da kudurin neman tsige Mista Zuma, bayan kotun kolin kasar ta yanke hukuncin cewa shugaban ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, saboda ya ki ya biya miliyoyin daloli na gwamnati da ya kashe wajen gyaran gidansa.

A 'yan kwanakin da suka wuce, wasu manyan 'yan jam'iyyar ANC ta Mista Zuman ma, sun bukace shi da ya yi murabus.

Karin bayani