Facebook zai ba masu makanta damar 'ganin' hotuna

Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Ana sanya hotuna biliyan daya da miliyan dari takwas kowace rana a shafukan sada zumunta.

Shafin Facebook zai kaddamar da wani tsari da zai rika tantance hotuna tare da sanar da masu matsalar makanta irin yadda hotunan su ke a zahiri.

Ko a watan daya gabata ma shafin Twitter ya sanya wani abu makamancin wannan da ke ba masu amfani da shafin bayyana irin yadda hotunan su suke.

An kiyasta cewa ana sanya hotuna kimanin biliyan daya da miliyan dari takwas kowace rana a shafukan sada zumunta kamar su Twitter da Instagram da Facebook.

A halin yanzu dai masu makanta dai na amfani ne da wata na'ura mai suna screenreaders wajen iya amfani da kwamfuta inda na'urar ke sauya abubuwan da aka rubuta zuwa murya don sauraro ga masu makanta.