US: Trump ya sha kasa a zaben fid-da-gwani

'Yan takarar shugabancin Amurka na jam'iyar Republican Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan takarar shugabancin Amurka na jam'iyar Republican

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyar Republican , Sanata Ted Cruz ya kayar da Donald Trump a zaben fid-da-gwani a jihar Wisconsin.

Ana kallon sakamakon na Wisconsin a matsayin wani zakaran gwajin dafi ga Mr Trump, wanda yakin neman zaben sa a cikin makonnin da suka gabata ya kasance cikin rudani, bayan wasu kalamai da ya yi game da mata, da suka hada da mai dakin Mr Cruz.

A zaben fid-da-gwani na jam'iyar Democrat, Bernie Sanders ya kayar da abokiyar karawarsa , Hilary Clinton, duk kuwa da cewa bai kai yadda zai hana mata daukacin tagomashin da take da shi ba.