South Africa: Zuma na fuskantar tsigewa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gidan da Jacob Zuma ya gina ne ya jawo masa matsala.

Jagoran jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, Mmusi Maimane, ta Afrika ta Kudu, ya ce dole ne 'yan majalisar ƙasar su zaba tsakanin kundin tsarin mulki da shugaba Jacob Zuma.

A ranar Talata ne dai 'yan majalisar za su tafka mahawarata tsige shugaba Zuma ko kuma ƙyale shi ya ci gaba da mulki.

Amakon da ya gabata ne babbar kotun kasar ta yanke hukuncin cewa Mista Zuma ya yi wa tsarin mulkin kasar karan tsaye, saboda kashe miliyoyin daloli da ya yi a kan ginin gidansa.

Ana dai tunanin cewa yunkurin tsige Jacob Zuma ka iya fuskantar cikas daga bangaren jam'iyyar ANC mai mulki wadda take da rinjaye a majalisar.

Da ma Mista Zuma ya fadi cewa idan dai har za a tsige shi to fa dole ne a rushe ita ma majalisar.