Za a yi mahaukaciyar guguwa a Fiji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Fabrairu ma guguwar ta ratsa ta Fiji inda ta yi barna

Fiye da mutane dubu shida a kasar Fiji sun bar gidajensu, inda suka koma zama a wuraren neman tsira, yayin da suke sa rai da zuwan mahaukaciyar guguwa hade da ambaliyar ruwa ta Cyclone Zena.

Har yanzu dama, kasar ta Fiji ba ta gama farfadowa daga barnar da bala'in guguwar Cyclone Winston ta yi a kasar ba, wacce ake gani ita ce guguwa mafi karfi da aka taba fuskanta a Kudancin Pacific.

Fiye da mutane 40 ne suka mutu lokacin da guguwar ta Cyclone Winston ta ratsa a watan Fabrairu.

Har yanzu wasu mutanen kasar na zama ne a wurare na wucin gadi, lamarin da yasa yanzu suka fi kasancewa cikin hadarin guguwar da ke tafe.