Shirin Sanin kai 2016: Makafi na iya ganin hotuna a shafin Facebook

Image caption Na'urar na iya bayyana hotunan abubuwa da dama, kamar bishiyoyi da ciyayi.

Duba da yadda hotuna ke cigaba da mamaye yanar gizo, shafin muhawara na Facebook ya kaddamar da wani tsari da ke iya "karanta" hoto ya kuma bayyana wa makafi abin da hoton ke nunawa.

Shafin intanet na sauyawa, inda daga amfani da rubuce-rubuce yanzu an koma yawanci da hotuna ake amfani.

A kalla mutane biliyan 1.8 ne ke sanya hotuna a kullum a shafukan sada zumunta kamar su Twitter da Instagram da kuma Facebook.

Wannan abin farin ciki ne ga masu son daukar hoto, amma kuma ga makafi, ba abu ne mai dadi ba, tunda ba iya gani suke ba, duk kuwa da cigaban da aka samu ta fannin fasaha.

To amma yanzu wannan sabon shiri da Facebook ya kaddamar ranar Talata, na kokarin kawo mafita.

Makafi na amfani da wata na'ura mai suna Screenreaders, domin su iya amfani da komfuta, wanda ke bayyana masu rubuce-rubuce da sautin murya, amma kuma ban da hotuna.

Amfani da na'urar Artificial Intelligence(AI), zai bai wa Facebook damar gano sirrin bayyana hotuna da aka sanya, ta yadda na'urar Screenreader za ta iya karantowa da sautin murya.

Kamfanin Facebook ya ce yanzu ya horar da na'urorinsa domin su rika gane sirrin bayyana abubuwa da ayyuka kusan 80, wadanda suke hadawa da kwatance.

Na'urar tana kara inganta da yawan sirrin hotuna da ta bayyana, ga kuma ire-iren abubuwan da na'urara ke iya fassarawa:

Ababan hawa - Mota da Jirgin ruwa da Jirgin sama da Keke da Babur da Jirgin kasa da bas-bas da ma titi.

Muhalli - Waje da Tsaunuka da bishiya da kankara da gajimari da rafi da bakin teku da ruwa da igiyar ruwa da rana da kuma ciyayi.

Wasanni - Tennis da Iyo da Filin wasanni da Kwallon kwando da wasannin golf.

Hakkin mallakar hoto Facebook

Abinci - Ayis kirim da suchi da pizza da kayan zaki da kofi.

Tufafi - Jariri da madubin ido da gemu da murmushi da kayan kawa da takalma da kuma daukar hoto da kanka watau selfie.

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption (Daga hannunka na hagu) Ma'aikacin Facebook Matt King da Jeffery Wieland da Shaomei Wu, wadanda suka yi aikin na'urar ta AI.

Matt King, injiniya ne ma'aikacin kamfanin Facebook, kuma wanda ya rasa idanuwansa sanadiyyar cutar idanuwa da ke bata kwayoyin halittar gani mai suna retinitis pigmentosa, shi ne ya kirkiro da wannan na'ura.

"Akwai abubuwa da dama da ke faruwa a Facebook wanda sai da idanu ake gani," In ji King.

Ya kara da cewa, "Amma idan kuma har kai makaho ne, sai ka ga an bar ka a baya."

Wannan na'urar da King da abokan aikinsa suka kirkiro, na amfani ne da wata na'urar da ke gane sirrin bayyana abubuwa na hoto, an kuma tsarata ta yadda za ta gane abubuwa kamar abinci da ababan hawa.