Angola ta bukaci tallafi wajen IMF

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Angola ce ta biyu a Afrika, wajen fitar da man fetur.

Kasar Angola ta bukaci Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF, da ta tallafa mata bayan ta fuskanci faduwa a kudaden shiga sakamakon faduwar farashin man fetur.

Fitar da man fetur shi ne ashi 95 cikin dari na lalitar kudin shiga na kasar, kazalika fiye da kashi biyu bisa uku na kudin da gwamnatin kasar ke samu.

A wata sanarwa da ministan kudin kasar ya fitar, ya ce gwamnati za ta yi aiki kafada-da- kafada da IMF, domin inganta tattalin arziki Angola.

Ana sa ran kulla yarjejeniyar cikin wannan watan na Afrilu.

Angola ce kasa ta biyu a Afirka, cikin mafiya safarar mai zuwa kasuwannin duniya, kuma ta fuskanci matsalar tattalin arziki saboda faduwar farashin man.