Nigeria: 'Kowa sai ya biya haraji a Kaduna'

Hakkin mallakar hoto kaduna govt
Image caption Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta yi haka ne a kokarin da ta ke yi na kara hanyoyin samun kudin shiga a jahar.

A Najeriya, gwamnatin jihar Kaduna ta bullo da wata sabuwar hanya ta karbar haraji mai suna 'presumptive Tax'.

Gwamnatin jahar ta ce ta bullo da tsarin ne domin karbar haraji a hannun masu kananan sana'o'i,wadanda a baya ba sa biyan haraji.

Shugaban hukumar tattara kudin shiga ta jahar Alh Muktar Ahmed ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta yi haka ne a kokarin da ta ke yi na kara hanyoyin samun kudin shiga a jahar.

Raguwar kudaden dake zuwa jahar daga aljihun gwamnatin tarayya ce ta sanya jahar Kaduna neman hanyoyin samun kudin shiga don yin ayyuka ga jama'a.