Ƙarancin mai ya jawo rashin wuta a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Niger tana samun wuta daga Najeriya.

Matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da ita a Najeriya, ta shafi makwabciyarta, jamhuriyar Nijar.

A wata sanarwa da hukumar wutar lantarkin jamhuriyar Niger, NIGELEC, ta fitar, shiyyoyi bakwai daga cikin takwas na ƙasar sun yi fama da ƙarancin wuta har na kwana uku.

Niger dai tana samun kusan kaso 70 na wutar lantarki ne daga makwabciyarta Najeriya, duk kuwa da cewa ita ma tana da nata albarkatun man fetur da kuma na Uranium.

Wata ƙididdiga da Babban Bankin Duniya ya fitar ta nuna ƙasa da kaso 15 na 'yan Niger ne suke samun wutan lantarki saboda talaucin da ƙasar take fama da shi.