Yadda 'yan Nigeria ke jin matsalar mai

Image caption Mutane dai na kwana a kan layukan mai.

A Najeriya, matsalar karancin man fetur da tsadarsa na ci gaba da jefa jama'a cikin mawuyacin halin rayuwa.

Kasar dai ta kwashe watanni da dama tana fuskantar matsalar ta ƙarancin man fetur daga lokaci zuwa lokaci.

Shin ko a wane irin hali al'ummar ƙasar ke ciki sakamakon matsalar ta man fetur wadda taƙi ci taƙi cinyewa?

Saurari ra'ayin wasu masu ƙananan sana'o'i, a jihar Bauchi, a hirarsu da wakilinmu, Ishaq Khalid, domin jin halin da suke ciki.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti