Sudan: Sai 2020 zan bar mulki — al Bashir

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Omar al-Bashir ya hau mulki a 1989

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da kotun ICC ke tuhuma kan laifukan yaki ya ce zai sauka daga kan karagar mulki a shekara ta 2020.

Hakan shi zai kai shi ga cika shekaru 31 a kan karagar mulki.

Sai dai wasu masu sharhi na cewa a baya ya sha fadin cewa zai sauka daga mulkin amma daga bisani yana karya alkawari.

A wata hira da BBC shugaba Bashir ya musanta zargin da ake yi masa kan aikata cin zarafin da dakaraun kasar ta Sudan suka aikata a wani sabon fada da ya barke a yankin Jebel Marra na Darfur cikin wanannn shekarar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da miliyan biyu da rabi ne suka rasa matsugunansu a Darfur tun a shekara ta 2003, kana fiye da dubu dari a cikin wannan shekarar tun bayan da sojojinsa suka fara kai farmaki a Darfur.