Aikawa da bidiyo kai tsaye ta Facebook

Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Za'a rika amfani da wannan hanya ta IOS da wayoyin tafi da gidanka

Shafin Facebook ya bullo da wata hanya ta aikawa da bidiyo da ake dauka ta wayar tafi-da-gidanka kai tsaye tare da samun martani daga wadanda aka tura wa bidiyon.

Za a rika amfani da wannan hanya ta IOS da wayoyin tafi-da-gidanka inda masu amfani za su iya tura bidiyo na duk wasu abubuwan da ke gudana.

A shekarar da ta gabata ne aka kaddamar da wannan tsari inda aka ba jama'a damar fara amfani da shi a Amurka a watan Janairu yayin da a wasu kasashe aka fara amfani da shi a watan Fabrairu.

Masu amfani da wannan tsari dai za su iya gayyatar abokansu don su kalli bidiyo kai tsaye tare da su, kuma za su iya kallon martanin da abokan ke cewa game da bidiyon.