Zika: Amurka ta kara zage damtse

Hakkin mallakar hoto
Image caption An gano ana iya daukan cutar ta Zika ta hanyar zamantakewa, kazalika yana haddasa gilu a jarirai.

Fadar shugaban Amurka, White House ta ce ta na sake kebe kusan dala miliyan 590, don taimakawa wajen yaki da barazanar cutar zazzabin Zika, wacce ke sa ana haihuwar jarirai masu kananan kai, watau gilu.

Wani kakakin fadar ta White House, ya ce wannan yunkuri, wani mataki ne na wucin gadi na samar da kudaden binciken magunguna.

Dubban mutane ne suka kamu da cutar ta Zika wacce sauro ke yadawa.

An bayar da rahoton bullar cutar a fiye da kasashe 20, akasari kasashen yankin Latin Amurka.