Chad: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga

Image caption Masu zanga-zanga na dauke da hotunan masu fafutukar da ake tuhuma

<span >

<span >'Yan danda a Chadi sun tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga wadanda suka yi dafifi a gaban kotu da ke babban birnin kasar Ndamena ranar Alhamis, ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da harbin iska.

Masu zanga-zangar sun taru ne domin nuna adawa da cigaba da tsare wasu masu fafutuka hudu da ake yi, wadanda suka bayyana a gaban kotun inda ake tuhumarsu da tunzura mutane don nuna adawa da takarar shugabancin kasar da Idriis Deby ya tsaya a karo na biyar.

Masu fafutukar da suka gurfana a gaban kotun na daga cikin jigogin wata kungiya da ke koarin ganin sun dakatar da shugaba Deby tsayawa takarar.

A wannan karo ma alkali ya dage zaman kotun zuwa ranar Alhamis mako mai zuwa.

Image caption A baya-bayan nan ma masu zanga-zanga suka yi ta hura usur a Chadi don nuna adawa da Deby

Ko da yake kuma lauya mai kare gwamnati ya bukaci da kotu ta daure su na tsawon watanni shida a gidan yari.

A ranar 10 ga watan Afrilu ne za a yi zaben shugaban kasa a Chadi, inda shugaba mai ci Idris Deby zai tsaya takarar karo na biyar, bayan shafe shekaru 26 yana mulki.