Djibouti na zaben shugaban kasa

Zaben na yau, zai gudana ne bayan an shafe mako guda ana tayar da jiyoyin wuya kuma jam'iyyun bangaren adawa su ka yi ta korefe-korafe.

Shugaba Ismael Omar Guelleh wanda ke kan kujerar mulkin kasar, na neman wani sabon wa'adi a karo na hudu, inda kuma ya ke fuskantar hamayya mai tsanani daga 'yan takara biyu na bangaren adawa da suka hada da Omar Elmi Kaireh da kuma Mohamed Daoud Chehem.

To sai dai masu nazarin lamura a kasar na cewa 'yan takarar biyu na bangaren adawa ba su da karfi kuma sun samu baraka tsakaninsu.

Shugaban kasar dai ya hau kujerar mulkin tun shekarar 1999 kuma shi ne shugaba na biyu da kasar ta yi tun bayan samun 'yan cin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Faransa a shekara ta 1977.